Tunatarwa:
Tare da
Shaikh Ibrahim Zakzaky

Imanin Abu Dalib ingantaccen abu ne ta fuskar hankali da ruwaya

In ji Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky

A lokacin da Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky yake gabatar da tafsirin Aya ta 56 cikin Suratul Kasas, inda Allah Ta’ala yake fadin cewa; “Innaka la tahdi man ahbabta walikannallah yahdi man yasha'u” watau “Lalle kai ba ka shiryar da wanda kake so, amma Allah ne yake shiryar da wanda ya so”, ya bayyana cewa wannan Aya tana nuna yadda Manzon Allah (S) yake kaunar Kuraishawa da su yi imani ne, amma kuma su suna bijirewa, kamar yadda a wani waje Allah Ta’ala yake cewa game da yadda Manzon Allah (S) yake damuwa game da shiryuwar mutane yana cewa: “Ka kusa da ka halaka kanka saboda ba su yi imani ba...”. Shi ya sa a nan Allah Ta’ala yake lallashin sa, yana ce masa kai ba za ka iya sa mutum ya yi imani ba, Allah ne yake shiryar da su.

Sannan sai Shaikh Zakzaky ya kawo yadda wasu ke nuna cewa sanadiyyar saukar wannan Aya shi ne wai yayin da wafati ya zo wa Abu Dalib, wai sai Manzon Allah ya je masa yana cewa ka ce “la’ilaha illah, in yi maka shaida gaba ga Allah ranar alkiyama.” Sai wai shi kuma ya ce, “ba zan fadi wannan kalma ba, saboda kada manyan Kuraishawa su yi mini dariya, su ce saboda na ga zan mutu ne shi ya sa na karbi imani.” Sai wai ya cika ba shi da imani, shi ya sa Manzon Allah (S) ya kasance yana damuwa, sai Allah Ta’ala wai ya saukar da wannan Aya yana ce masa “Lalle kai ba ka shiryar da wanda kake so, amma Allah ne yake shiryar da wanda ya so.”

Malam ya nuna cewa sam wannan magana ba ta da asali a Musulunci, saboda na farko dai galiban wadanda suke mutanen kirki ne su a jahiliyya sune suka yi imani da wannan Manzon lokacin da ya bayyana. Wannan kuwa hatta a wajen Ammah suna da Hadisi wanda yake nuna cewa “Zababbenku a jahiliyyah, zababbenku a Musulunci idan ya zama Malami.”. To, a nan ana iya cewa shi Abu Dalib wane laifi ya yi ta yadda ya zama ya kasa imani da wannan Manzon bayan bayyanarsa, kasancewar ya kare shi fiye da yadda yake kare ’ya’yansa na cikinsa?

Ko kuwa goyon bayan da ya yi ta nuna masa ta yadda hatta kafiran Kuraishawa sun kasa kai wa zuwa gare shi da cutarwa har sai bayan da ya yi wafati shi ne laifinsa?

A lokacin da Abu Dalib ya rasu bayan wafatin Ummul Mumineen Khadijah matar Manzon Allah (S) kafirai sun yi bushara, sannan suka yi biki suka sha giya suka ce yanzu babu mai kare shi (Manzon Allah). Daga nan ne sai Allah Ta’ala ya yi wa Manzon Allah (S) umurni da ya yi hijira daga Makka zuwa Madina.

Bayan da Malam ya kawo wannan shimfidar ne sai ya gutsuro kadan daga cikin irin abin da tarihi ya bari kan imanin Abu Dalib, bayan ya tunatar kan abin da ya taba bayyanawa a shimfida a baya game da imanin na Abu Dalib.

Shaikh Zakzaky a wancan lokacin kimanin shekaru biyu da suka gabata yayin da yake tafsirin suratu-Taubah ya yi magana mai dan tsawo kan imanin Abu Dalib, inda ya dauko Hadisai daga Littafin Kafi na Shaikh Kulaini da kuma sharhinsa a littafin Mir’atul Uqul, ya yi bayani mai tsawo kan yadda musuluntar Abu Dalib ta kasance. Da yardar Allah, kamar yadda Malam ya so, nan gaba kadan za a mayar da wannan bayanin a cikin dan karamin littafi ya shiga hannun jama’a.

BAYANI KAN MUSULUNTAR ABU DALIB DA WANDA YA RUWAITO LABARIN CEWA YA CIKA BA SHI DA IMANI

Tun da farko dai shi Abu Dalib ya karbi Manzon Allah (S) ne daga Abdul Muddalib Kakan Manzon Allah (S) ne a matsayin wasiyya, wato wasiyya Mahaifinsa Abdul Muddalib ya yi na ya rike Manzon Allah (S), saboda shi Abdul Muddalib kamar yadda tarihi ya nuna ya riga ya san cewa jikansa Annabi ne tun yana dan yaro karami.

Ya zo a tarihi cewa Abdul Muddalib yakan zaunar da Manzon Allah (S) a kan wani matashi a tsakanin manyan Kuraishawa a lokacin zamansu na majalisa, har su dattawan sukan ce masa me ya sa yake irin wannan alhali? Wannan yaro ne? Sai ya ce musu ai wannan ba yaro bane, shi ne Shugabanmu duka.

To, ya tabbata a lokacin da Abdul Muddalib ya zo mutuwa ya kira Abu Dalib ya ba shi rikon Manzon Allah (S) ya ce masa ga amana nan, ba ni da wani wasiyyar da zan bar maka fiye da wannan, kuma shi wannan shi ne Annabin karshe.

Kuma hakika Abu Dalib ya kasance yana nuna kauna ga Annabi (S) fiye da yadda yake son ’ya’yansa, kuma ya ba shi kariya ta dukkanin yadda yake iyawa.

Dukkanin wadannan ruwayoyi sun zo ne daga tushen Ammah suna cikin littafan Ahlul Sunnah Wal Jama’ah, duk Malamansu sun san da su.

Amma a ruwayar Ahlul Bait (AS) wadanda suka fi kowa sanin abin da ya faru lokacin rasuwar Abu Dalib, sun bayyana yadda musuluntar Abu Dalib ta kasance.

MUSULUNTAR ABU DALIB A RUWAYAR IYALAN GIDAN MANZON ALLAH (S).

A lokacin da aka yi wa Manzon Allah (S) wahayin farko a Kogon Hira yana tare da Amiral Mumineen Ali (AS) a lokacin ya ga haske ya cika kogon gaba dayansa.

A lokacin Imam Ali (AS) ya ji dukkanin abin da Manzon Allah (S) ya ji, kuma ya ga dukkanin abin da Manzon Allah (S) ya gani, sai dai shi ba Annabi bane.

A lokacin da Mala’ika Jibril ya zo ya yi wa Manzon Allah (S) sallama, sannan ya sumbanci goshinsa, ya ce masa wa’adi ya yi yanzu kuma lokacin aiko ka ya yi, sannan sai ya karanta masa suratu Ikra’a.

Bayan sun fito daga Kogon Manzon Allah (S) yana tafiya tare da dan Amminsa, Imam Ali (AS), babu wata itaciya da za su wuce, ko dutse, da dukkanin halitta face sai sun yi gaisuwa ga Manzon Allah (S) sun ce masa “Assalamu alaika Ya Rasulullah!” Yayin da ya iso gida sai matarsa Khadija ta zo ta gan shi cike da haske, sannan ya ce mata an riga an yi wahayi, ya kira ta ga kalmar shahada, ta ce masa dama ta dade da sanin wannan, sannan ta yi imani, sannan sai ga Abu Dalib ya zo yana cewa, “ya dana an riga an yi maka wahayin ne?” Ya ce, “lalle Baba an yi.”

Sannan ya yi imani ya ce “Alhamdullahi ban mutu ba sai da na ga wannan lokacin.”

Sannan ne sai ya ce masa, “ya dana nuna mini Aya wadda zan tabbatar an yi maka wannan wahayin? Ya ce wace Aya kuma kake nema? Ba ka yi imani bane? Sai ya ce na yi, amma don zuciya ta natsu”.

Sannan sai Manzon Allah (S) ya ce, “to wace Aya kake so, sai ya nuna masa wata bishiya ya ce ka kira wannan bishiyar ta zo ta shaida cewa kai Manzon Allah ne”. Sai Manzon Allah ya yi hakan. Ya kira bishiya ta tugo daga tushenta ta zo gabansa ta yi masa sallama, sannan ta ce lalle kai Manzon Allah ne.

A wani bangare na bayaninsa, Malam ya yi magana kan wanda ya ruwaito labarin cewa Abu Dalib ya mutu ba shi da imani, wato Mugirah Ibnu Shu’ubah, wanda ya musulunta ne shekara ta takwas bayan hijirar Manzon Allah (S), sannan kuma shi mutumin Da’if ne Bathaqafe. To, abin tambaya a nan shi ne yaya zai yiwu mutumin Da’if a wancan lokacin zai san da rasuwar wani mutum a Makka har ya zo ya shaidi abin da zai faru a lokacin?

Shi Mugirah shi ne wanda Mu’awiyya ya nada Gwamnan Kufa bayan yarjejeniyar da Mu’awiyya ya yi da Imam Hassan (AS). Kuma shi ne ya sunnanta tsine wa Imam Ali (AS) a mumbari. Saboda haka nan makiyin Imam Ali (AS) ne, shi ne kuma ya kawo wannan ruwayar wadda take nuna cewa Abu Dalib mahaifin Imam Ali (AS) bai musulunta ba.

Wasu daga cikin waki’o’in da suka auku a cikin watan Ramadan

Daga www.harkarmusulunci.org

A wannan shekarar Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky bayan ya kammala gabatar da tafsirin da ya saba gabatarwa a kowace rana yana ware wasu ’yan mintoci a karshe ya kawo bayani kan wasu daga cikin abubuwan da suka faru.

Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a cikin watan Ramadan wadanda suka hada da mutuwar wasu fitattun fajiran bayi da kuma wasu daga cikin manyan bayin Allah nagargaru.

WAFATIN SAYYIDAH NAFISAH AL-HUSSAINIYYAH

Ita dai wannan babbar baiwar Allah da aka yi ta a tarihi, ’yar Hasan ce, dan Zaid, dan Imam Hasan (AS), dan Imam Ali Ibn Abi Dalib (AS).

Mahaifiyarta ita ce Fatimah daga cikin zuriyar Abul Fadl Abbas. An daura auren Hasan mahaifin Nafisah da Fatimah mahaifiyarta ce a Karbala, saboda haka nan iyayenta suna daga cikin wadanda bayan kashe Imam Husaini (AS) aka ribace su, a matsayin fursunonin yaki.

WAFATINTA A FARKON WATAN RAMADAN

Ita Sayyidah Nafisah ta zauna a Masar ne, ta auri Ishaq Al-mutaman dan Imam Ja’afar Assadiq (AS), ta kasance mace ce wadda ake nunawa a matsayi na martaba a Zuhudu, ta kasance tun a lokacin tana raye ta haka kabarinta, tana shiga ciki tana karatun Alkur’ani da sauran ibadodi, a ciki take kammala karatun Alkur’ani mai tsarki.

Ta yi wata rashin lafiya a cikin watan Rajab har ta kai ma ta rubuta wa mijinta a lokacin yana Madina tana bayyana masa halin da take ciki na rashin lafiya, da kuma yadda ciwon ya yi mata tsanani.

An bayyana cewa wata rana lokacin tana cikin wannan ciwo sai Likita ya halarce ta ya kawo mata abinci da magani da rana a kan ta ci wannan abincin, sannan kuma ta sha magani, sai ta ce: “Shekaru 30 ina rokon Allah kar ya dauki raina face ina Azumi, sannan bayan dukkanin wannan sai a yau in ci abinci?” Saboda haka nan dai ba ta ci wannan abincin ba, sai ta rika karanta Alkur’ani cikin suratul An’am har ya zuwa lokacin da ta kai ayar da Allah Ta’ala yake cewa: “Lahum Darus-salami inda Rabbihim”, wato “suna da gidan aminci a wajen Ubangijinsu”. Sai ta cika ta koma ga rahamar Ubangijinta”.

HUBBAREN SAYYIDAH NAFISAH YANA MASAR INDA AKE ZIYARAR TA:

A lokacin da mijinta ya sami labarin wafatin ta lokacin yana Madina sai ya nemi ya dauko gawar ta daga Masar ya zo da ita Madina don ya rufe ta a wajen kakanninta a makabartar Baki’ah da ke birnin Manzon Allah (S), Madina.

Amma sai mutanen Masar suka roke shi suna neman alfarma a kan ya bar ta a can Masar din, to bayan haka ta auku sai shi Ishak Al-mu’taman ya yi mafarki da Manzon Allah (S) yana gaya masa cewa: “Kada ka saba wa mutanen Masar cikin wannan lamari, saboda albarkacin Nafisah Allah Ta’ala zai saukar da rahamarsa da albarkatunsa a garin su”. To saboda haka nan sai aka rufe ta a nan inda ta haka kabarin ta kafin rasuwarta.

HALAKAR ZIYAD DAN BABANSA

A rana ta hudu ga watan Ramadan shekara ta 53 bayan hijira waki’ar halakar Ziyad Dan Babansa ta auku.

WANENE ZIYAD DAN BABANSA:

Shi dai Ziyad Dan Babansa, haka nan aka fi saninsa a tarihi, sai dai a wani lokaci an rika kiran sa Ziyad Ibn Ubayy.

A lokacin da Abdullah Ibn Abbas ya taso daga Basra lokacin yana Gwamnan Imam Ali (AS) a can, don ya zo wajen Amiral Mumineen ya yi masa jajen kashe Muhammad Ibn Abibakar, sai ya wakilta Ziyad Ibn Ubayy a Basra, shi kuma Mu’awiyyah bayan ya ji labarin yanzu Abdullah Ibn Abbas ya baro Basra sai ya tura wata runduna da makamai su kame Basra su mayar da ita karkashin ikonsa.

To amma sai shi Ziyad ya hada wasu jama’a aka je aka yake su aka kore su, sannan bayan Ibn Abbas ya dawo sai ya mika masa komai.

Tun bayan wannan lokacin Mu’awiyyah ya yi ta son ya ga ya jawo Ziyad ya koma bangarensa, sai wata rana ya aiko masa cewa shi Mu’awiyyah da Ziyad ubansu daya ne, har ma ya turo ’yar uwarsa ya ce ta kwaranye gashin kanta a gabansa domin kuwa shi muharraminta ne.

Saboda haka nan sai ya yarda da hakan, kuma daga nan sai aka rika kiransa Ziyad Ibn Abi-Sufyan. Tun daga nan sai ya yi bara’ah ga Imam Ali (AS) ya rika azabtar da mabiyansa, da nau’o’in azabtarwa daban-daban ciki har da kashe jarirai da huda cikuna, da kona gidaje. Shi ne ya kashe Abdurrahman Ibn Hasan ta hanyar bisne shi da ransa, saboda yana nuna kauna ga Amiral Mumineen Ali (AS).

Haka nan kuma a Basra da Kufa ya kashe magoya bayan Imam Ali (AS) dubu 13, saboda bayan mutuwar Mugirah Ibn Shu’ubah, Mu’awiyyah ya nada shi (Ziyad) Gwamnan Kufa.

Akwai lokacin da ya ce a tattara mutane gaba dayansu za a bi su layi-layi ko dai ka tsine wa Imam Ali (AS) ka yi masa bara’ah, ko kuma a kashe ka. Bayan mutane sun taru ana jiran Sarki ya fito bai fito ba, sai daga baya aka shiga aka tarar ya mimmike yana karkarwa mutuwa ta je masa, haka nan Ziyad Dan Babansa ya halaka. Allah ya tsine masa da dukkanin ire-iren sa.

MUTUWAR MARWAN IBN HAKAM

Mutuwar Marwan Ibnul Hakam tana daya daga cikin waki’o’i da suka auku a cikin watan Ramadan, ya mutu ne kamar yadda wasu suka ruwaito ranar 3 ga watan Ramadan shekara ta 65 bayan hijira, a garin Damashq. An sassaba dangane da yawan shekarunsa a duniya a lokacin da ya mutu, wasu na cewa 61, wasu kuma na cewa 81.

Ya zama Khalifah ne na tsawon watanni tara kawai.

WANENE MARWAN IBNUL HAKAM:

Ana yi wa Marwan Ibnul Hakam Ibnu Abil As-lakabi da cewa shi ne “Wazag Ibnul Wazag”, wato “Tsaka Dan Tsaka”, saboda kamar yadda ya zo a Hadisin Manzon Allah (S) cewa ita Tsaka fasika ce. Haka nan kuma an ruwaito cewa Manzon Allah (S) ya la’ance su shi da mahaifinsa, sannan ya kore su daga birnin Madina.

Ummil Mumineen A’isha, matar Manzon Allah (S) ta taba gaya wa Marwan cewa: “Lalle Manzon Allah (S) ya taba tsine maka kai da mahaifinka a lokacin kana cikin tsatsonsa”. Wannan abu ya faru ne a lokacin da shi Marwan din yake kan mumbarin Manzon Allah (S) a Madina, saboda bayan korar su da Manzon Allah (S) ya yi a lokacin rayuwarsa, sai a lokacin Khalifancin Uthman Ibn Affan ya dawo da su Madina, kuma ya nada shi Marwan din a matsayin babban Wazirinsa, kuma Sakatarensa. Sannan a lokacin Mu’awiyyah Ibn Abi Sufyan ya nada shi Gwamnansa a Madina.

Har ila yau kuma Uthman ya ba shi Khumusin Ifrikiyyah tun daga Tarabulus har zuwa wani gari da ake kira Danja, wanda yake cikin Morocco a yanzu. Haka nan kuma ya ba shi Fadak wannan dukiya da Manzon Allah (S) ya bai wa ’yarsa Fatimah (SA) tun lokacin yana raye.

Haka nan kuma shi ne ya kashe Dalha da kibiya a lokacin yakin Jamal, kuma wanda Imam Ali (AS) ya ce masa ba ya bukatan mubaya’arsa, saboda ko da ya yi mubaya’ar sau 20 ne zai karya.

SANADIYYAR MUTUWARSA

Bayan da ya zama Sarkin Musulmi sai ya auri tsohuwar matar Yazidu, kuma ita ce ta zama sanadin mutuwarsa, ta sanya masa guba a abinci ya zama kurma, sannan bayan haka nan ta sa matasai ta toshe bakinsa ta zauna a kai ita da kuyanginta, har sai da ya cika.

HARIN TABUKA

Daga cikin abubuwan da suka auku a cikin watan Ramadan, akwai harin Tabuka. Kamar yadda ya zo a tarihi ya auku ne a cikin watan Ramadan shekara ta tara bayan hijirar Manzon Allah (S) daga Makka zuwa Madina.

SANADIYYAR WANNAN HARI:

A lokacin da Rumawa suka shirya kawo hari Madina kuma suka sha alwashin kashe Manzon Allah (S) da kuma gamawa da addinin gaba daya, sai Manzon Allah (S) ya umurci gaba dayan Muminai da yin shiri don yakar su, har Manzon Allah (S) ya bayyana cewa: “Ba a daukewa kowa da ya yi imani da Allah da Manzonsa ba wajen zuwa wannan hari na Tabuka, wannan shi ne harin Tabuka wanda aka yi shekara ta tara bayan hijira kamar yadda muka ambata.

Haka nan kuma ita ce karshen yaki ko kuma hari wanda Manzon Allah (S) ya yi a rayuwarsa.

SUNAYEN DA AKE KIRAN HARIN TABUKA DA SU A TARIHI:

Ya tabbata a tarihi ana kiran wannan hari na Tabuka da sunaye, daga ciki ana kiran sa da Gazwatul Fadhiha, wato hari mai tonawa (Kunyatawa). Saboda wannan hari ya tona asiran wasu daga cikin munafukai a Madina, a sanadin wannan hari ne aka gano wasu Sahabbai 82 wadanda suka kawo uzurori mara sa tushe na karya na kin zuwan su harin na Tabuka wanda Allah Ta’ala ya ambace su da cewa su Rijsun ne, wato kazanta ne su, kuma makomar su jahannama, amma kasantuwar sun yi sarauta a lokacin rayuwarsu, sun kasance manyan mutane ba a fadin sunayensu, alhali kuma duk an san su.

Haka nan kuma wannan harin ya tona asirin wasu da suka yi shirin kashe Manzon Allah (S) ta yadda suka shirya cewa taguwar sa za ta taka wasu tsakwankwani da suka sa a wani falalin dutse a lokacin dawowarsa daga Tabuka, ta yadda bayan taguwar ta taka sai ta zame ta fado kasan gadar daga nan sai ya rasu.

A lokacin da taguwar Manzon Allah (S) ta zo wajen sai kawai aka ganta tana tafiya a iska ba tare da ta taka wadannan tsakwankwanin ba.

Ta haka nan ne Allah Ta’ala ya tsamakar da bawan sa Manzon Allah (S), sannan kuma ya tona asirin su wadannan munafukan.

Haka nan kuma suka yi da Imam Ali (AS) a lokacin da ya taso da dokinsa don ya tari Manzon Allah (S) a lokacin dawowar sa daga Tabuka, inda suka haka rami, sannan suka sanya tabarma a kai ta yadda idan dokin Imam Ali ya zo wajen zai taka sai ya fada ciki shi ma ya mutu shi kenan sun huta.

Amma shi ma Imam Ali (AS) Allah ya kare shi ta yadda a lokacin da dokinsa ya zo wajen sai aka ga ya sanya kofatonsa yana tattaka wajen da tabarmar take har ya zuwa lokacin da ta fada sai aka gano abin da ya faru, sannan sai Imam Ali (AS) ya kauce ya tsira daga wannan dasisa.


Shafin Farko