DAGA WAKILANMU
Kar mu zama ’yan rakiya a Harkar nan
In ji Malama Zeenatu Ibrahim Daga Aliyu SalehMalama Zeenatu Ibrahim ta hori ’yan uwa mata da su zama wadanda ake gudanar da wannan Harkar tare da su, ba wadanda suke raka majensu wajen gudanar da al’amuran Harka ba. “Ya zama ana yin Harkar tare da mu ne, ba wai mu zama ’yan rakiya ba.”
Malama Zeenatu Ibrahim, wacce ke yin jawabi a wajen taron Mu’utamar na wuni guda da ’yan uwa mata suka shirya a Husainiyya Bakiyyatullah, Zariya ranar Lahadin makon jiya, ta bayyana cewa; “Makasudin shirya shi wannaan taron na Mu’umatar ga ’yan uwa mata shi ne domin kwakkwafa tunanin juna game da abin da ya wajaba a kanmu”.
Ta ci gaba da cewa; “Idan har mutum yana yin rakiya, fima labudda idan an kai wani waje zai dawo. Idan ka yi bako ka raka shi, ai dole ka dawo ko? Amma idan tafiyar kanka kake yi fa? Ka ga za ka yi ta tafiya ne har sai ka cimma inda kake son zuwa”.
Malama Zeenat ta hakikance cewa dalilin kirkiro wannan taron da ake yi lokaci bayan lokaci shi ne saboda an lura akwai wasu ’yan uwan da suke zama ’yan rakiya a wannan Harkar; “Kodayake ba cikin ’yan uwa mata kawai ake samun wannan matsala ba, maza da mata suna da wannan matsala. Wasu kawai za ka ga ana tafiya da su, amma kamar ba su san inda aka sa gaba ba. A kan haka ne sai muka ga cewa ya doru a kanmu mu ga cewa su ’yan uwa mata sun samar da wani fage wanda za mu rinka tunanin juna. Babban makasudin wannan zaman ke nan. Don ya zama muna da fikira, kuma mun san me ya sa muke yin wannan Harkar, kuma mun san me ya kamata mu yi”.
Bugu da kari ta ce, a cikin wannan hanyar da muka kama akwai wasu alamomi da ke nuna mana cewa mutum yana kan hanyar bai kauce ba, akwai kuma wasu abubuwa da ake yi wadanda wasu suke ganin su kamar kanana ne, alhali a wajen Allah manya ne, abubuwa ne da ke rusa ayyuka, ko da kuwa mutum yana kwana Salla, yana wuni Azumi da karatun Alkur’ani. “Idan ya zama kana yin wadannan abubuwan za ka zube a gaban Allah”.
Malama Zeenat Ibrahim ta jawo hankalin ’yan uwa game da muhimmancin dauriya a tafarkin Allah, inda ta kafa hujja da Hadisin Imam Sadik (AS) da ke nuna muhimmancin dauriya a tafarkin Allah. Ta tunatar da ’yan uwa abubuwan da ke faruwa a wasu garuruwan kamar Gombe da kuma wani masallaci a Unguwar Alkali da ke Zariya. “Idan aka dage shi ne zai zama silar samun nasara”.
Ta ce; “Malam bai boye mana komai dangane da wannan Harkar ba, ya gaya mana cewa idan har muka ce La ilaha Illallah, abin da ya samu na farko, mu ma zai same mu. Ta hanyar da Allah yake daga darajar bayinsa shi ne ta hanyar jarabawa. Idan kuma ya sanya maka ibtila’i, abin da yake so kawai shi ne ka daure. Me ya kamata ka roki Allah? Shi ne dauriya. Amma ba za ka ce kar ya kawo bala’i ba, in bai kawo ba, ba za ka samu daukaka ba. Ba za ka roki Allah ya kawo bala’i ba, domin idan ya zo karshenta ba za ka daure ba. Abin da ya kamata ka roki Allah shi ne dauriya da juriya”.
Malama Zeenat ta bayyana cewa duk wadanda ake ba mu labarinsu masu dauriya suna da komai irin namu. An jarraba su, amma kuma sun daure. Allah ne ya taimake su suka daure. “Mun sani idan Allah zai yi amfani da mu wajen tabbatar addini za mu sha wahala, amma kuma idan wahalar ta zo, Allah ya ba mu dauriya. Amma ba a cewa kar a ja maka waki’a. Idan ba ka son waki’a, to ka bar Harkar mana”.
Ta ce, akwai hanyoyi da dama wajen neman tabbata a tafarkin Allah, amma babba daga cikin su shi ne kyawawan dabi’u da kuma ibadoji, musamman Sallar dare ta fi wahala, amma idan mutum ya fara yi kuma Allah ya taimake shi, zai rika jin dadinta. Akwai kuma karatun Alkur’ani, wanda zai zama akalla a wata mutum yana sauke Alkur’ani. Akwai kuma addu’o’i da dama da mutum zai lizimta. “Manzon Allah (S) ya ce wanda ya fi makwabtaka da shi a ranar lahira shi ne wanda ya fi kyawawan dabi’u”, ta ce.
Tun da farko da take nata jawabin a wajen taron, Malama Khadija Mustafa Kabir Malumfashi, ta jawo hankalin ’yan uwanta mata ne a kan su zage damtse wajen ibada da neman kusanci da Allah. Ta ce, Manzon Allah (S) ya fada cewa a lokacin da ya je Isra’i da Mi’iraji ya ga mafi yawan ’yan wuta mata ne. “Saboda haka wallahi aiki ne ja a gare mu don kare kanmu daga wannan. Wajibi ne mu yawaita ibadoji da kuma kyawawan dabi’u”. Malama Khadija ta koka matuka da irin halaye na rashin ya kamata da ke faruwa a tsakanin wasu Sistocin, ta ce ba a hada sabon Allah da neman yardar Allah. Ta ce kashi 80% ta nasarar da Marigayi Imam Khumaini ya samu daga Sistoci ya same ta; “Ba ma fatan mu taimaki Malam haka?”
Ta hori ’yan uwa mata a kan su sa a cikin zuciyarsu a kan za su taimaki Malam. “Kowa ya ji a jikinsa cewa ita wannan da’awar kamar daukar jinka ce, ita kuma jinka mutum daya bai daukar ta, kowa da irin gudummawar da zai bayar wajen ganin Harkar ta kai ga gaci. Wajibi ne ki yi tunani ke wace irin baiwa Allah ya ba ki da za ki taimaki wannan Harkar?”
Malama Khadija Mustafa ta koka matuka da irin Sistocin nan da suka jima a cikin Harkar nan, amma kuma ba su san komai dangane da abubuwan da ake gudanarwa ba. Saboda mafiya yawansu idan an zo taron surutu suke yi ba sa jin abin da ake gabatarwa, kuma idan sun koma gida ba su bibiyar abubuwan da aka yi ba.
Ta jawo hankalin Sistoci game da al’adar nan da aka san mata ita ta yawaita gulma da kuma karairayi gami da gutsiri-tsoma. “Domin Manzon Allah (S) ya ce, Mumini ba ya karya. Idan har ke mumina ce bai kamata bakinki ya fadi karya ba. Wajibi ne mu guji gulma. Duk wanda ya kawo maki tsegumi da gulma ba masoyinki ba ne. Manzon Allah (S) ya ce, a lokacin da kake gulmar mutum tamkar namansa kake yaga danye kake ci.”
Malama Khadija Mustafa ta bai wa ’yan uwa matan da suke wajen wata dabara da za su yi wajen maganin magulmaci, da kuma yadda za a yi maganin makaryaci da hanyar da mutum zai bi ya zama mai gaskiya da rikon amana. Ta jawo hankalinsu game da wajibcin bai wa yara tarbiyya ta addini. “Bai kamata a ga mai gwagwarmayar addini yana yin wadannan miyagun dabi’u ba. Duk abin da muka san idan mun yi shi zai nisanta mu da Allah, mu bar shi, duk wanda muka san idan mun yi za mu samu kusanci da Allah, mu yi kokari mu aikata shi, wannan kuma shi ne kololuwar hadafin kiran Malam”.
Ta jawo hankalin ’yan uwa su sa ido sosai a kan ’ya’yansu, musamman wadanda suke makarantun gaba da firamare. Ta nuna matukar damuwarta a kan yadda wasu iyayen ke ce wa ’ya’yansu idan sun je makarantu su rinka boye kansu. “Duk da cewa kowa ya san wannan da’awar daga makarantu ta faro, ban san a ina suka samo wannan tunanin na yin takiyya a makarantu ba? Wani lokacin a kokarinsu na boye kansu, sai kuma su je su narke, su zama wani abu daban”.
Harisawa sun gabatar da Maulidin Shehu Dan Fodiyo a Kaduna
Daga Aliyu Saleh A ranar Juma’ar nan da ta gabata ne, ’yan uwa Harisawa suka gabatar da kwarya-kwaryar taron Maulidin Shehu Usman Dan Fodiyo, inda Malam Mukhtar Sahabi ya gabatar da jawabi a wajen.
A cikin jawabin da ya gabatar a wajen taron da aka gudanar da shi a harabar masallacin Layin Kosai da ke Tudun Wada Kaduna, Malam Mukhtar Sahabi, ya jawo hankalin al’ummar Musulmi game da muhimmancin tuntuntuni dangane da al’amarin Shehu Dan Fodiyo da kuma kara yin riko da tafarkinsa. “Abin takaici ne a kan yadda aka mantar da mutane Shehu Dan Fodiyo”.
Malam Sahabi, wanda ya nuna damuwarsa matuka a kan yadda al’ummar Musulmi suka yi watsi da karantarwar Shehu Dan Fodiyo, ya tabbatar da cewa da za a dabbaka karantawarsa, da al’ummar Musulmi sun dawo da izzar da suke da ita a da. Ya ce; “Halin da al’ummar Musulmi ke ciki a wannan lokacin sakamakon barin tafarkin Shehu ne”.
Ya yi nuni da cewa duk hakan ya biyo bayan irin makida da makircin da Turawan mulkin-mallaka, wadanda suka ci mu yaki ne suka kulla, har ya zama sun rarraba Daular Usmaniyya zuwa kasashe don su ji dadin yi masu mulkin-mallaka. “Mu muna alfahari ne da tarihinmu, idan muka bari aka raba mu da tarihinmu an gama da mu ke nan”.
Malam Sahabi ya yi tilawar tarihin Shehu, kama daga rayuwa, karatu, jihadi da kuma yadda ya gudanar da da’awarsa da kuma irin kulen da ya fuskanta yayin isar da sakon. Ya ce kuma duk wanda ya kama tafarkin Shehu, sai ya gamu da makamancin abubuwan da ya hadu da su.
Da ya waiga a kan irin karatu da kuma halayen Shehu Dan Fodiyo, Malam Mukhtar Sahabi, ya bayyana cewa ba ma shi Shehun ba, hatta kaninsa Abdullahi Fodiyo, ya kasance mutum ne mai himma da hamasa wajen kokarin ibada da bahasi a cikin al’amarin addini. Ya ce wata rana Muhammad, dan Shehu ya ga yadda ake tsananin girmama Abdullahi, sai ya je gidansa ya kwana, sai ya ga abubuwan mamaki game da shi. Malam Sahabi ya bayyana irin yadda a shekaru sama da 30 Allah ya tayar da Sayyid Zakzaky yana kira irin na Shehu Dan Fodiyo, yana fuskantar irin kulen da ya fuskanta, sakamakon yadda yake tafiya a kan irin tafarkinsa. “Har makarantunmu ma ya sa masu suna Fudiyya ne don a koyar da yara Fodiyanci (irin aikin da Shehu Dan Fodiyo ya yi). Dan Fodiyo ya wuce, dole ne ka san dan Fodiyon zamaninka”, in ji shi.
A lokacin da yake bayani a madadin wadanda suka shirya taron, Alhaji Sani Mai Shadda, ya bayyana cewa Sayyid Zakzaky ne ya umurci Harisawa a duk inda suke su gudanar da irin wannan mamakancin taron a ‘unit’ dinsu. Ya ce wannan shi ne karo na hudu da suka gabatar a wannan ‘unit’ din.
An gudanar da taron Yaumu Arba’in a Funtuwa
Daga Husaini Baba
’Yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na garin Funtuwa, sun gabatar da taron Yaumu Arba’in na Imamu Husaini (AS), inda Wakilin ’yun uwa na garin, Malam Rabi’u Abdullah ya gabatar da jawabi.
A jawabin nasa, Malam Rabi’u ya bayyana irin darussan da ya kamata ’yan uwa su dauka game da shi kansa juyayin na Ashura. Inda ya bayyana cewa, Sahabin Manzon Allah (S) Jabir Bin Abdullahi ne ya fara ziyarar Arba’in na Ashura a Karbala, kuma shi ne ya assasa share fagen tunawa da Ashura. Ya kuma ce, waki’ar Karbala ba abu ne wanda zuciya za ta manta da shi ba, haka ma ziyarar Ashura na kara motsa radadin abin da ya faru a lokacin Ashura.
Malam Rabi’u Abdullahi ya kara da cewa, duba rayuwar Imam Husaini (AS) yana nuna cewa ba za a yi addini ba ne idan za a kwana lafiya, Musulunci ana aikata shi ne da dadi ko ba dadi, da hadari ko ba hadari, don haka ziyarar Arba’in tana tuno dukkan abin da ya faru a kan Imam Husaini (AS) ne.
Malamin ya kara da cewa, waki’ar Ashura cin riba ce ga addini domin masu rubutun tarihi sun bayyana cewa, jini ya yi nasara a kan makami, saboda an yi amfani da makami an kashe bayin Allah, wadanda ba su da makamai, an shekar da jinainansu kuma shekar da jinin ne ya jawo nasara.
Ya ce; “Kuma ba na tunanin a ce wani ya fito fili ya ce shi yana goyon bayan Yazidu a kan abin da ya yi, amma tsakanin dan Shi’a da wanda ba danShi’a ba za ka ga suna nuna takaicin abin da ya faru kan Imam Husaini (AS), kuma abin da Imam Husaini (AS) ya yi shi ne addinin Musulunci, kuma ya nuna cewa Musulunci shi ne fito-na-fito da fajirai makiya addinin Musulunci”.
Malam Rabi’u ya bayyana cewa, darasin Ashura gaba dayansa ne nuna wa mutane bore da bijirewa, da kuma dakewa don tabbatar da cewa mutum ya samu hakkinsa, kuma ya cimma burinsa. Ya kuma ce, babban burin Mumini bawan Allah shi ne ya yi abin da Allah Ta’ala zai yarda da shi. Wannan na nuna cewa, kowane irin karfi ne za ka iya tunkarar sa, don tabbatar da wannan hadafin naka. Ya ce, in mutum na karkashin mulkin azzalumai, bijirewa da jajircewa da kuma dakewa shi ne babban makamin da kowa ya kamata ya yi aiki da shi. Ya ce, mai neman ’yanci ne ko mai neman addini ne. “Kuma ba ka da abin da ke ba da ’yanci illa addinin Musulunci”, in ji shi.
A karshe, Malamin ya bayyana cewa ya zama wajibi mu gode wa Allah da falarar da ya yi mana ta chanyar Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) da bin tafarkin Iyalan Gidan Annabi (S) da kuma rokon Allah ya tabbatar da mu a kan bin jagorancinsa. “Ga su kuma jama’a, ya kamata su gane cewa tafarkin tsira shi ne amsa kiran Sayyid Zakzaky, don shi ne mafita ke hannunnsa, ba wadannan azzaluman ba”, ya karkare.
Tijjaniyya da Shi’a uwa daya uba daya suke
In ji Shaikh Abu Ubaida Maigatari
Daga Sani Babandi Maigatari (sanibabandi@ymail.com)
Mashahurin Malamin addinin Musulunci nan da ke garin Maigatari a Jihar Zamfara, Shaikh Abu Ubaida ya tabbatar da cewa Darikar Tijjaniyya da Shi’a uwa daya uba daya suke.
Shehin Malamin, wanda kuma shi ne Shugaban Darikar Tijjaniyya na garin Maigatari, ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsar tawagar ’yan uwa na Dandalin Matasa da suka ziyarce shi ranar Arba’een na Imam Husaini (AS) da nufin jajanta masa game da da ta’addancin da aka yi masu a Karbala.
Shaikh Abu Ubaida ya ci gaba da cewa; “Abin da ya sa na ce haka shi ne Shaikh Ahmad Tijjani wanda ya kafa Darikar Tijjaniya Jika ne ga Imam Hasan (AS) domin abin da ya kawo Kakannin Shehu Tijjani Maroko, an sami wani gurbataccen yanayi ne, wato lokacin Khalifancin Ma’awiyya Bin Abu Sufyan, wanda ya nuna kiyayya da gaba da Iyalan Annabi (AS), abin da ya sa uka bar Madina suka koma Maroko”
Shehin Malamin ya ci gaba da bayyana cewa mutum zai sami lada a ziyara, wanda duk ibadarsa ba zai kai shi girma da yawa ba. Ya kuma ce duk wanda ya kama hanya domin ziyara Allah zai sa Mala’iku dubu 70 su raka shi suna nema masa gafara a wajen Allah.
Ya ci gaba da cewa Imam Ali (AS) shi ne na hudu a jerin Sahabbai manya, amma in dai daukaka ce da daraja a gurin Allah shi ne na daya a cikin Sahabbai, kuma duk wanda yake so ya ga irin cin mutunci da wulakanci da aka yi wa Imam Husain (AS), to ya je ya duba littafin Nurul Absar.
Ya ce duk ibadarka in dai ba ka son Iyalan Gidan Annabi (S), to ba za ka shiga Aljanna ba, inda ya yi wa ’yan uwa fatan Allah ya tabbatar da su a wannan hanya ta biyayya ga Ahlul Baiti (AS).
Tun da farko Malam Tukur Wada Ahmad ya ce sune ’yan uwa na Dandalin Matasa na Harka Islamiyya wacce take karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky, “Mun kawo wannan ziyarar ne bisa irin tarbiyyar da muka samu daga Jagoranmu”.
Dan uwa Malam Ahmad Mukhtar ya yi wa Malamin bayani dangane da makasudin kawo wannan ziyarar tasu, inda ya ce; “Makasudin kawo wannan ziyara tamu shi ne domin arba'een na Imam Husain domin neman tabarruki da albarka da hikimar da Allah ya kimsa a cikin arba'eena din”.
Ya kara da cewa; “A cikin irin wannan ranar ce kuma Jabir Bin Abdullah Al-ansary ya ziyarci Imam Husain (AS), kuma a irin wannan ranar ce kan Imam Husain (AS) ya koma ga gangar jikinsa, kuma mun yi tawassuli da wannan hikimar da Allah ya kimsa a cikin arba'een din. Don haka muka shirya wannan musamman domin mu jajanta wa juna a bisa abin da ya sami Iyalan Gidan Annabta (AS)”.
Yajin aikin ma’aikata: ISMA ta kai dauki asibitin Tsafe
Bayan shiga yajin aikin ma’aikatan kasar nan, a karon farko hadin gwiwar ’yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky na bangaren kiwon lafiya ISMA da Dandalin Matasa na garin Tsafe sun kai daukin gaggawa ga majiyantan da ke kwance a babban Asibitin gwamnati domin bai wa marasa lafiya tallafi, kamar yadda a kullum Sayyid Zakzaky ke ta kiran ’yan uwa a kai.
Tawagar ma’aikatan sun kunshi ’yan uwa maza da mata tare da kayan aiki, inda ’yan uwa mata suka tafi wurin majinyata mata, su kuma maza suka tafi wurin maza domin ba da tallafin kamar yadda aka tsara. Tawagawar na karkashin jagoranci Malam Muhammad Liman.
Wakilinmu ya shaidi yadda wannan aiki ya gudana a sashen maza a ranar farko zuwa rana ta uku. Da isar ’yan uwa nan take suka ci gaba da duba majinyata tare da yi masu aiki a kan matsalolinsu daban-daban.
Habibu Lawali Nasarawa dan kimanin shekara 10 ne, ya samu karaya da kuma wani rauni kusa da karayar, ya kwana biyu ba a duba shi ba, ko da wannan tawagar ta isa kafar yaron har ta fara ruwa tare da wari, amma cikin ikon Allah an samu shawo kan matsalar yaron a sanadiyyar taimakon da ’yan uwa suka ba shi.
Amadu Tambai Sungawa magidanci ne kuma yana dauke da wani mumunan rauni a kafa bayan hatsarin da ya samu da mashin, kuma yana cikin jinya aka shiga wannan yajin aiki, ya shaida wa Wakilinmu cewa; “Inda na kara kwana biyu ba tare da an duba wannan kafar ba, da mai yuwa in rasa ta baki daya, amma sanadiyyar almajiran Malam Zakzaky na samu taimako, kullum sai son zo sun wanke mani ita tare da yi mani allurai da sauransu. Don haka babu abin da za mu ce wa Malam Zakzaky da almajiransa, sai mu ce mun gode, Allah ya kara ba su kariya da daukaka a kan makiyansu”.
Daga nan ’yan agajin sun sallami wasu daga cikin majinyatan wadanda aka yi wa aiki (threater) bayan sun warware masu dinki tare da rubuta masu magunguna da kuma fada masu abubuwan da ake so su kiyaye bayan sun je gida kamar yadda ake bukata. A sashen mata ma haka abin yake domin a nan ma ’yan uwa mata sun taka muhimmiyar rawa ga mata majinyata, inda suka dudduba su tare da yi masu abin da suke bukata.
Kafin tawagar ta bar Asibitin sai da suka gabatar da share-share a cikin dakunan majinyata. Ya zuwa lokacin da nake hada wannan rahotun ’yan uwan na ci gaba da gudanar da wannan aiki na kula da majiyanta a Asibitin ta Tsafe.
Malama Atika Sulaiman na daga cikin ’yan uwan da suka gudanar da wannan aikin, kuma ta shaida wa Wakilinmu dalilin fituwarsu; “Mun fito ne bisa umurnin Jagoranmu Sayyid Ibraheem Zakzaky, domin shi ne ya ba mu wannan umurni cewa duk lokacin da aka samu matsala irin wannan, mu fito mu taimaka wa jama’a, domin hakan kan taimaka wurin ragewa al’umma radadin halin da muke ciki a kasar nan”.
Lawali Amadu daga kauyen Nasarawa Mai Fara na daga cikin masu jinyan ’yan uwansu a lokacin da ’yan uwa suka kai wannan daukin, ya yi godiya mai yawa a kan wannan namijin kokari na kai masu dauki da aka yi. Ya roki Allah da ya ji kan Mahaifan Sayyid Zakzaky.
Shahidin Masallacin Juma’a, Usman Bello Gombe
Daga Mu’assasatus Shuhada na yankin Ja’afar Dayyar
An haifi Malam Usman Bello ne a wani gari da ake ce wa Njaba a yankin Gashuwa cikin jihar Yobe a shekarar 1966. Daga baya suka dawo shi da babansa garin Abujayel cikin garin Bajoga a jihar Gombe. A nan ne kuma Marigayi Malam Usman ya yi karatunsa a gaban Alaramma Malam Umaru. Ya yi shekara 1 Babansa ya yi masa aure.
Bayan dawowar Malam Muhammad Adamu Abbari Gombe ne, sai Shahid Usman Bello shi ma ya dawo Gombe saboda kamar yadda ya taba fada ya dawo Gombe ne ba don neman kudi ba, sai don neman shiriya a hannun Malam Muhammad Adamu Abbare. Ya zauna ne a Tudun Wadan Jauro Abare a Gombe, inda yake noma yake kuma aikin leburanci a wani gidan buga bulo.
Malam Usman Bello ya yi shahada ne a ranar Laraba 26/1/1433 (21/12/2011) a masallacin Juma’a na Kofar Sarkin Gombe. Abin ya samo asali ne tun ranar Litinin 23/1/1433 inda Sarkin Gombe, Dakta Usman Shehu Abubakar ya gayyaci ’yan Kalare (‘yan daba) karkashin jagorancin Sarkin Lema, Ardo Chindo suka far wa ’yan uwa a cikin masallacin a yayin da suke gabatar da karatun Ta’alim da suka saba yi sama da shekaru 20.
Nan take aka raunata ’yan uwa takwas, daga cikinsu akwai Shahid Usman Bello. Ya koma gida da rauni. Lokacin da matarsa ta tamabaye shi, sai ya ce mata an far mana a masallaci ne, amma kada ki damu ba na jin radadi, ba na jin komai. Washegari Talata ya je aikinsa a gidan bulon, ya wuni yana aikinsa ba matsala.
A ranar Laraba ya yi niyyar zuwa Kurugu domin ya ziyarci Babansa wanda yake kwance ba shi da lafiya, sai ya ce bari ya fara da ziyartar ’yan uwa da suka jikkata a waki’ar Litinin, sannan daga baya ya je Kurugu.
Ya yi wanka, da ya zo fita sai iyalinsa ta ce masa yau ma za ku je masallacin ne? Kar fa a kashe ku, sai shi Shahid din ya ce mata: “Ina nema mana Aljanna ne, kada ku ji tsoro, in na yi shahada ’yan uwa za su kula da ku”. Sai ya yi bankwana da su ya fita. Da yake shi Haris ne ya je zaman Harisawa aka raba aiki, an ce kuma ’yan uwa su yi Sallar La’asar a masallacin. Daga nan shi Shahid ya kama hanya ba tare da bata lokaci ba ya nufo masallaci.
Kafin a yi Sallah ’yan Kalare sun cika harabar masallacin, a nan suka fara dukan ’yan uwa da suka soma zuwa. Shi Malam Usman Bello shi ma yana cikin masallacin, sai ’yan Kalaren suka fara dukansa da sanda, sai wani Bafade ya zo daga gidan Sarki ya ga ana dukan Shahid din, sai ya ce dan Shi’a ne ko? To, maza ku kashe shi! Daga nan ne fa sai wani ya daba masa wuka a wuya har wukar ta lume a ciki. Wani ya shaida mana cewa wani dan Kalare da ake ce wa Abdulmalik (Mali) dan unguwar kasuwar Mata Layin Najmuddin ne ya kashe shi.
An kashe Malam Usman Bello a gaban jami’an tsaro, sojoji da ’yan sanda. Bayan caka masa wukan ne sai ’yan sanda suka dauke shi jina-jina suka jefa shi a motarsu suka tafi da shi. A ran nan an raunata ’yan uwa 28. Daga baya sai aka bincika sai ba a ga Malam Usman Bello ba, aka yi ta neman sa amma ba same shi ba.
Washegari ranar Alhamis an je duk ofisoshin ’yan sanda, amma duk inda aka je sai su ce su babu kowa a hannunsu. Sai da aka shafe mako guda ana neman sa, amma shiru ba same shi ba. Sai a ranan Laraba, bayan mako guda da aukuwar al’amarin aka je mutuware na Asibitin Gombe ana cigiya. Sai masu jiran mutuwaren suka ce lallai akwai gawawwaki uku na wasu da ba a san masu su ba. Ana bude na ukunsu sai ga Shahid Usman Bello a kwance jini na zuba a jikinsa. Fuskarsa alamar yana murmushi, jikinsa bai kumbura, kafarsa sanye da takalminsa. Mai jiran mutuwaren Kirista ne, amma sai da ya yi mamakin yadda ya ga ga shi an kashe mutum mako guda, amma ga jini na zuba kamar a lokacin aka kashe shi.
An yi jana’izarsa ne ranar Juma’a 30/l2/2011 a kofar fada na Gombe, kuma har zuwa ranar Juma’ar jini bai daina zuba a inda aka soke shin ba, sai da aka samu auduga aka toshe wajen, kuma duk gabobinsa an jujjuya su kamar yadda ake yi wa rayayye, fuskarsa ta kara haske, hakoransa sun yi fari tas. An lullube shi da likkafani na Jaushanul Kabir da aka rubuta da Turbar Karbala.
Daruruwan mutane ne suka halarci Sallar Shahid din wanda Malam Muhammad Abbari ya jagoranta. ’Yan uwa daga Zariya, Kano, Darazo da sauran Da’irorin yankin Gombe da sauran al’ummar Musulmi suka yi Sallar. Bayan yin Sallar ne aka shiga sahu ’yan uwa maza da mata a yayin da Harisawa suke gaba suna buga badujala suna fareti suna wakokin yabon Shahidi, har aka je makabarta ta hanyan Bajoga wacce ta kai tsawon kilomita shida daga cikin gari, amma haka aka je da kafa cikin sahu.
Masu gadin makabartan sun ce su tun da suke ba su taba ganin jama’a haka sun rako wata gawa ba, kuma ba su san ana yi wa gawa gata ba sai a ranar. Malam Muhammad Adamu Abbari ya yi jawabi inda yake cewa lallai an kawo rayayye ne cikin matattu. Bayan gama binne shi ne dai sai aka nemi infaki a wurin inda aka tara sama da dubu 25 aka bai wa masu gadin makabartar duk albarkacin Shahid Usman Bello.
Malam Usman Bello dai ya yi shahada ya bar mace daya (Malama Hawwa) da yara shida: Adamu 16, Zainab 14, Yunusa 11, Fatima 8, Ali 5, da Hadiza 3, dukkansu suna Gombe.
