Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



DAGA WAKILANMU

Fudiyya Rigasa ta gudanar da taron kara wa juna sani

Daga Musa Muhammad Awwal

Ranar Asabar din makonjiya ne, Madrasatul Fudiyya Rigasa, Kaduna ta gudanar da wani taron kara wa juna sani na yini guda ga Malaman makarantar na fannin boko da na addinin Musulunci don zaburantar da su a aikin nasu na koyarwa.

Taron, wanda aka gudanar a babban dakin taro na makarantar, Wakilinmu da ya halarta ya shaida mana cewa Malamai ne wadanda suka hada da maza da mata, da ma shi kansa Shugaban makaranta suka samu halarta. Sannan kuma Malamai masana kan harkar koyarwa ne suka gabatar da kasidu a wurin.

Cikin kasidar da ya gabatar mai taken ‘Malami, koyarwa da dabi’un kwararren Malami’, Malam Saminu Muhammad Unguwar Mu’azu, Kaduna, ya fara ne da bayyana abubuwan da ya kamata a yi la’akari da su wajen daukar Malami mai koyarwa.

Masani kan harkar koyarwar ya ce, yana da matukar muhimmanci a samu mutum yana da sha’awar koyarwar, sannan kuma mutum ya kasance yana da cikakken horo da cikakkun takardu a fannin koyarwa, sannan kuma wajibi ne Malami ya zama masani a kan abin da zai koyar.

Malam Saminu, ya kuma bayyana cewa duk da yake Malamai sun bambanta a fannoni da dama wadanda suka hada da kabila, addini, yanki, jinsi da dai sauransu, to amma ya jaddada cewa wajibi ne a samu Malami da natsuwa, tare da sanin abin da zai koyar, hanyar da zai bi wajen koyarwa, da kuma bin bahasin yadda daliban nasa ke fahimtar koyarwar da yake masu.

Haka kuma Malamin ya bayyana wasu mihimman siffofi da ya wajaba a ce Malami yana da su, wadanda suka hada da natsuwa, gaskiya, sadaukarwa, mutunci, mai hadiye fushinsa, taka-tsantsan wajen horo ga dalibai, wato kada a tsananta, kada kuma a yi sako-sako.

Da yake bayani game da yanayin da ya kamata makaranta ta kasance kuwa, Malam Saminu Muhammad, ya bayyana cewa wajibi ne a samar da ajujuwan karatu masu kyau da tsafta, yalwatattun kujeru da sauran kayan koyarwa, kayan wasannin motsa jiki, natsuwa da rashin hayaniya a makaranta da dai sauransu.

Shi ma a cikin tasa kasidar, Shugaban Lajnar Fudiyya na Kaduna, wanda yake shi ma masani ne a wannan fanni, Malam Aliyu Tirmiziy, ya bayyana cewa yana da matukar muhimmanci a samu fahimtar juna tsakanin Malami da dalibansa.

Ya ce samun fahimtar juna tsakaninsu zai matukar taimaka wa Malami domin samun yanayin koyarwa, sannan zai taimaka wa dalibi ya samu natsuwa da mayar da hankali wajen sauraron abin da ake koya masa. Ya ce, sannan kuma hakan zai taimaka wa dalibi wajen samun fahimtar abin da Malamin ke koya masa.

Malam Tirmiziy ya ci gaba da cewa, haka kuma yana da kyau Malami ya zama yana mai nuna natsuwa ga dalibinsa, haka shi ma dalibi ya zama mai biyayya da da’a ga Malaminsa.

Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban wannan makaranta, Malam Umar Aliyu, ya bayyana cewa sun fito da wannan taro ne domin kara ilimantar da Malaman nasu game da abin da ya shafi koyarwa. Ya ce duk da yake dai Malaman nasu kwararru ne a harkar, amma Bahaushe ya ce ‘in kana da kyau ka kara da wanka.’

Don haka sai Shugaban marantar ya ce, wannan shi ne karo na farko na wannan taro, amma za su ga cewa ya kasance taro ne da za a rinka gudanar da shi lokaci-lokaci.

Da yake bayyana jin dadinsa game da taron da aka shirya masu, daya daga cikin Malaman da suka amfana da wannan horo, Malam Yakubu Haruna, ya nuna cewa ya ilimantu a abubuwa da yawa a wannan taro, musamman ta yadda za su kara samun himma da kwazo a harkar tasu ta koyarwa.

Saboda haka sai ya yi fatan cewa Hukumar makarantar za ta ci gaba da shirya masu irin wannan taro; “Lallai wannan taro zai taimaka matuka wajen kara sanar da Malaman hanyar koyarwa mai inganci,” in ji Malam Yakub.

Ita ma a nata tsokacin game da wannan taro, daya daga cikin Malaman makarantar, Malama Jamila Abba Khalil, ta bayyana cewa; “A gaskiya na yi matukar farin ciki da halartar wannan taro, domin tun da nake koyarwa a wannan makaranta ban taba halartar taro irin wannan ba, wanda ya ilimantar, ya kuma fadakar da ni ta kowane fanni, sai dai mu ce Alhamdulillah.”

Harisawa sun gabatar da Maulidin Shehu Dan Fodiyo a Kaduna

Daga Aliyu Saleh A ranar Juma’ar nan da ta gabata ne, ’yan uwa Harisawa suka gabatar da kwarya-kwaryar taron Maulidin Shehu Usman Dan Fodiyo, inda Malam Mukhtar Sahabi ya gabatar da jawabi a wajen.

A cikin jawabin da ya gabatar a wajen taron da aka gudanar da shi a harabar masallacin Layin Kosai da ke Tudun Wada Kaduna, Malam Mukhtar Sahabi, ya jawo hankalin al’ummar Musulmi game da muhimmancin tuntuntuni dangane da al’amarin Shehu Dan Fodiyo da kuma kara yin riko da tafarkinsa. “Abin takaici ne a kan yadda aka mantar da mutane Shehu Dan Fodiyo”.

Malam Sahabi, wanda ya nuna damuwarsa matuka a kan yadda al’ummar Musulmi suka yi watsi da karantarwar Shehu Dan Fodiyo, ya tabbatar da cewa da za a dabbaka karantawarsa, da al’ummar Musulmi sun dawo da izzar da suke da ita a da. Ya ce; “Halin da al’ummar Musulmi ke ciki a wannan lokacin sakamakon barin tafarkin Shehu ne”.

Ya yi nuni da cewa duk hakan ya biyo bayan irin makida da makircin da Turawan mulkin-mallaka, wadanda suka ci mu yaki ne suka kulla, har ya zama sun rarraba Daular Usmaniyya zuwa kasashe don su ji dadin yi masu mulkin-mallaka. “Mu muna alfahari ne da tarihinmu, idan muka bari aka raba mu da tarihinmu an gama da mu ke nan”.

Malam Sahabi ya yi tilawar tarihin Shehu, kama daga rayuwa, karatu, jihadi da kuma yadda ya gudanar da da’awarsa da kuma irin kulen da ya fuskanta yayin isar da sakon. Ya ce kuma duk wanda ya kama tafarkin Shehu, sai ya gamu da makamancin abubuwan da ya hadu da su.

Da ya waiga a kan irin karatu da kuma halayen Shehu Dan Fodiyo, Malam Mukhtar Sahabi, ya bayyana cewa ba ma shi Shehun ba, hatta kaninsa Abdullahi Fodiyo, ya kasance mutum ne mai himma da hamasa wajen kokarin ibada da bahasi a cikin al’amarin addini. Ya ce wata rana Muhammad, dan Shehu ya ga yadda ake tsananin girmama Abdullahi, sai ya je gidansa ya kwana, sai ya ga abubuwan mamaki game da shi. Malam Sahabi ya bayyana irin yadda a shekaru sama da 30 Allah ya tayar da Sayyid Zakzaky yana kira irin na Shehu Dan Fodiyo, yana fuskantar irin kulen da ya fuskanta, sakamakon yadda yake tafiya a kan irin tafarkinsa. “Har makarantunmu ma ya sa masu suna Fudiyya ne don a koyar da yara Fodiyanci (irin aikin da Shehu Dan Fodiyo ya yi). Dan Fodiyo ya wuce, dole ne ka san dan Fodiyon zamaninka”, in ji shi.

A lokacin da yake bayani a madadin wadanda suka shirya taron, Alhaji Sani Mai Shadda, ya bayyana cewa Sayyid Zakzaky ne ya umurci Harisawa a duk inda suke su gudanar da irin wannan mamakancin taron a ‘unit’ dinsu. Ya ce wannan shi ne karo na hudu da suka gabatar a wannan ‘unit’ din.

An gudanar da taron Yaumu Arba’in a Funtuwa

Daga Husaini Baba

’Yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na garin Funtuwa, sun gabatar da taron Yaumu Arba’in na Imamu Husaini (AS), inda Wakilin ’yun uwa na garin, Malam Rabi’u Abdullah ya gabatar da jawabi.

A jawabin nasa, Malam Rabi’u ya bayyana irin darussan da ya kamata ’yan uwa su dauka game da shi kansa juyayin na Ashura. Inda ya bayyana cewa, Sahabin Manzon Allah (S) Jabir Bin Abdullahi ne ya fara ziyarar Arba’in na Ashura a Karbala, kuma shi ne ya assasa share fagen tunawa da Ashura. Ya kuma ce, waki’ar Karbala ba abu ne wanda zuciya za ta manta da shi ba, haka ma ziyarar Ashura na kara motsa radadin abin da ya faru a lokacin Ashura.

Malam Rabi’u Abdullahi ya kara da cewa, duba rayuwar Imam Husaini (AS) yana nuna cewa ba za a yi addini ba ne idan za a kwana lafiya, Musulunci ana aikata shi ne da dadi ko ba dadi, da hadari ko ba hadari, don haka ziyarar Arba’in tana tuno dukkan abin da ya faru a kan Imam Husaini (AS) ne.

Malamin ya kara da cewa, waki’ar Ashura cin riba ce ga addini domin masu rubutun tarihi sun bayyana cewa, jini ya yi nasara a kan makami, saboda an yi amfani da makami an kashe bayin Allah, wadanda ba su da makamai, an shekar da jinainansu kuma shekar da jinin ne ya jawo nasara.

Ya ce; “Kuma ba na tunanin a ce wani ya fito fili ya ce shi yana goyon bayan Yazidu a kan abin da ya yi, amma tsakanin dan Shi’a da wanda ba danShi’a ba za ka ga suna nuna takaicin abin da ya faru kan Imam Husaini (AS), kuma abin da Imam Husaini (AS) ya yi shi ne addinin Musulunci, kuma ya nuna cewa Musulunci shi ne fito-na-fito da fajirai makiya addinin Musulunci”.

Malam Rabi’u ya bayyana cewa, darasin Ashura gaba dayansa ne nuna wa mutane bore da bijirewa, da kuma dakewa don tabbatar da cewa mutum ya samu hakkinsa, kuma ya cimma burinsa. Ya kuma ce, babban burin Mumini bawan Allah shi ne ya yi abin da Allah Ta’ala zai yarda da shi. Wannan na nuna cewa, kowane irin karfi ne za ka iya tunkarar sa, don tabbatar da wannan hadafin naka. Ya ce, in mutum na karkashin mulkin azzalumai, bijirewa da jajircewa da kuma dakewa shi ne babban makamin da kowa ya kamata ya yi aiki da shi. Ya ce, mai neman ’yanci ne ko mai neman addini ne. “Kuma ba ka da abin da ke ba da ’yanci illa addinin Musulunci”, in ji shi.

A karshe, Malamin ya bayyana cewa ya zama wajibi mu gode wa Allah da falarar da ya yi mana ta chanyar Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) da bin tafarkin Iyalan Gidan Annabi (S) da kuma rokon Allah ya tabbatar da mu a kan bin jagorancinsa. “Ga su kuma jama’a, ya kamata su gane cewa tafarkin tsira shi ne amsa kiran Sayyid Zakzaky, don shi ne mafita ke hannunnsa, ba wadannan azzaluman ba”, ya karkare.

Tijjaniyya da Shi’a uwa daya uba daya suke

In ji Shaikh Abu Ubaida Maigatari

Daga Sani Babandi Maigatari (sanibabandi@ymail.com)

Mashahurin Malamin addinin Musulunci nan da ke garin Maigatari a Jihar Zamfara, Shaikh Abu Ubaida ya tabbatar da cewa Darikar Tijjaniyya da Shi’a uwa daya uba daya suke.

Shehin Malamin, wanda kuma shi ne Shugaban Darikar Tijjaniyya na garin Maigatari, ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsar tawagar ’yan uwa na Dandalin Matasa da suka ziyarce shi ranar Arba’een na Imam Husaini (AS) da nufin jajanta masa game da da ta’addancin da aka yi masu a Karbala.

Shaikh Abu Ubaida ya ci gaba da cewa; “Abin da ya sa na ce haka shi ne Shaikh Ahmad Tijjani wanda ya kafa Darikar Tijjaniya Jika ne ga Imam Hasan (AS) domin abin da ya kawo Kakannin Shehu Tijjani Maroko, an sami wani gurbataccen yanayi ne, wato lokacin Khalifancin Ma’awiyya Bin Abu Sufyan, wanda ya nuna kiyayya da gaba da Iyalan Annabi (AS), abin da ya sa uka bar Madina suka koma Maroko”

Shehin Malamin ya ci gaba da bayyana cewa mutum zai sami lada a ziyara, wanda duk ibadarsa ba zai kai shi girma da yawa ba. Ya kuma ce duk wanda ya kama hanya domin ziyara Allah zai sa Mala’iku dubu 70 su raka shi suna nema masa gafara a wajen Allah.

Ya ci gaba da cewa Imam Ali (AS) shi ne na hudu a jerin Sahabbai manya, amma in dai daukaka ce da daraja a gurin Allah shi ne na daya a cikin Sahabbai, kuma duk wanda yake so ya ga irin cin mutunci da wulakanci da aka yi wa Imam Husain (AS), to ya je ya duba littafin Nurul Absar.

Ya ce duk ibadarka in dai ba ka son Iyalan Gidan Annabi (S), to ba za ka shiga Aljanna ba, inda ya yi wa ’yan uwa fatan Allah ya tabbatar da su a wannan hanya ta biyayya ga Ahlul Baiti (AS).

Tun da farko Malam Tukur Wada Ahmad ya ce sune ’yan uwa na Dandalin Matasa na Harka Islamiyya wacce take karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky, “Mun kawo wannan ziyarar ne bisa irin tarbiyyar da muka samu daga Jagoranmu”.

Dan uwa Malam Ahmad Mukhtar ya yi wa Malamin bayani dangane da makasudin kawo wannan ziyarar tasu, inda ya ce; “Makasudin kawo wannan ziyara tamu shi ne domin arba'een na Imam Husain domin neman tabarruki da albarka da hikimar da Allah ya kimsa a cikin arba'eena din”.

Ya kara da cewa; “A cikin irin wannan ranar ce kuma Jabir Bin Abdullah Al-ansary ya ziyarci Imam Husain (AS), kuma a irin wannan ranar ce kan Imam Husain (AS) ya koma ga gangar jikinsa, kuma mun yi tawassuli da wannan hikimar da Allah ya kimsa a cikin arba'een din. Don haka muka shirya wannan musamman domin mu jajanta wa juna a bisa abin da ya sami Iyalan Gidan Annabta (AS)”.

Yajin aikin ma’aikata: ISMA ta kai dauki asibitin Tsafe

Bayan shiga yajin aikin ma’aikatan kasar nan, a karon farko hadin gwiwar ’yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky na bangaren kiwon lafiya ISMA da Dandalin Matasa na garin Tsafe sun kai daukin gaggawa ga majiyantan da ke kwance a babban Asibitin gwamnati domin bai wa marasa lafiya tallafi, kamar yadda a kullum Sayyid Zakzaky ke ta kiran ’yan uwa a kai.

Tawagar ma’aikatan sun kunshi ’yan uwa maza da mata tare da kayan aiki, inda ’yan uwa mata suka tafi wurin majinyata mata, su kuma maza suka tafi wurin maza domin ba da tallafin kamar yadda aka tsara. Tawagawar na karkashin jagoranci Malam Muhammad Liman.

Wakilinmu ya shaidi yadda wannan aiki ya gudana a sashen maza a ranar farko zuwa rana ta uku. Da isar ’yan uwa nan take suka ci gaba da duba majinyata tare da yi masu aiki a kan matsalolinsu daban-daban.

Habibu Lawali Nasarawa dan kimanin shekara 10 ne, ya samu karaya da kuma wani rauni kusa da karayar, ya kwana biyu ba a duba shi ba, ko da wannan tawagar ta isa kafar yaron har ta fara ruwa tare da wari, amma cikin ikon Allah an samu shawo kan matsalar yaron a sanadiyyar taimakon da ’yan uwa suka ba shi.

Amadu Tambai Sungawa magidanci ne kuma yana dauke da wani mumunan rauni a kafa bayan hatsarin da ya samu da mashin, kuma yana cikin jinya aka shiga wannan yajin aiki, ya shaida wa Wakilinmu cewa; “Inda na kara kwana biyu ba tare da an duba wannan kafar ba, da mai yuwa in rasa ta baki daya, amma sanadiyyar almajiran Malam Zakzaky na samu taimako, kullum sai son zo sun wanke mani ita tare da yi mani allurai da sauransu. Don haka babu abin da za mu ce wa Malam Zakzaky da almajiransa, sai mu ce mun gode, Allah ya kara ba su kariya da daukaka a kan makiyansu”.

Daga nan ’yan agajin sun sallami wasu daga cikin majinyatan wadanda aka yi wa aiki (threater) bayan sun warware masu dinki tare da rubuta masu magunguna da kuma fada masu abubuwan da ake so su kiyaye bayan sun je gida kamar yadda ake bukata. A sashen mata ma haka abin yake domin a nan ma ’yan uwa mata sun taka muhimmiyar rawa ga mata majinyata, inda suka dudduba su tare da yi masu abin da suke bukata.

Kafin tawagar ta bar Asibitin sai da suka gabatar da share-share a cikin dakunan majinyata. Ya zuwa lokacin da nake hada wannan rahotun ’yan uwan na ci gaba da gudanar da wannan aiki na kula da majiyanta a Asibitin ta Tsafe.

Malama Atika Sulaiman na daga cikin ’yan uwan da suka gudanar da wannan aikin, kuma ta shaida wa Wakilinmu dalilin fituwarsu; “Mun fito ne bisa umurnin Jagoranmu Sayyid Ibraheem Zakzaky, domin shi ne ya ba mu wannan umurni cewa duk lokacin da aka samu matsala irin wannan, mu fito mu taimaka wa jama’a, domin hakan kan taimaka wurin ragewa al’umma radadin halin da muke ciki a kasar nan”.

Lawali Amadu daga kauyen Nasarawa Mai Fara na daga cikin masu jinyan ’yan uwansu a lokacin da ’yan uwa suka kai wannan daukin, ya yi godiya mai yawa a kan wannan namijin kokari na kai masu dauki da aka yi. Ya roki Allah da ya ji kan Mahaifan Sayyid Zakzaky.

Shahidin Masallacin Juma’a, Usman Bello Gombe

Daga Mu’assasatus Shuhada na yankin Ja’afar Dayyar

An haifi Malam Usman Bello ne a wani gari da ake ce wa Njaba a yankin Gashuwa cikin jihar Yobe a shekarar 1966. Daga baya suka dawo shi da babansa garin Abujayel cikin garin Bajoga a jihar Gombe. A nan ne kuma Marigayi Malam Usman ya yi karatunsa a gaban Alaramma Malam Umaru. Ya yi shekara 1 Babansa ya yi masa aure.

Bayan dawowar Malam Muhammad Adamu Abbari Gombe ne, sai Shahid Usman Bello shi ma ya dawo Gombe saboda kamar yadda ya taba fada ya dawo Gombe ne ba don neman kudi ba, sai don neman shiriya a hannun Malam Muhammad Adamu Abbare. Ya zauna ne a Tudun Wadan Jauro Abare a Gombe, inda yake noma yake kuma aikin leburanci a wani gidan buga bulo.

Malam Usman Bello ya yi shahada ne a ranar Laraba 26/1/1433 (21/12/2011) a masallacin Juma’a na Kofar Sarkin Gombe. Abin ya samo asali ne tun ranar Litinin 23/1/1433 inda Sarkin Gombe, Dakta Usman Shehu Abubakar ya gayyaci ’yan Kalare (‘yan daba) karkashin jagorancin Sarkin Lema, Ardo Chindo suka far wa ’yan uwa a cikin masallacin a yayin da suke gabatar da karatun Ta’alim da suka saba yi sama da shekaru 20.

Nan take aka raunata ’yan uwa takwas, daga cikinsu akwai Shahid Usman Bello. Ya koma gida da rauni. Lokacin da matarsa ta tamabaye shi, sai ya ce mata an far mana a masallaci ne, amma kada ki damu ba na jin radadi, ba na jin komai. Washegari Talata ya je aikinsa a gidan bulon, ya wuni yana aikinsa ba matsala.

A ranar Laraba ya yi niyyar zuwa Kurugu domin ya ziyarci Babansa wanda yake kwance ba shi da lafiya, sai ya ce bari ya fara da ziyartar ’yan uwa da suka jikkata a waki’ar Litinin, sannan daga baya ya je Kurugu.

Ya yi wanka, da ya zo fita sai iyalinsa ta ce masa yau ma za ku je masallacin ne? Kar fa a kashe ku, sai shi Shahid din ya ce mata: “Ina nema mana Aljanna ne, kada ku ji tsoro, in na yi shahada ’yan uwa za su kula da ku”. Sai ya yi bankwana da su ya fita. Da yake shi Haris ne ya je zaman Harisawa aka raba aiki, an ce kuma ’yan uwa su yi Sallar La’asar a masallacin. Daga nan shi Shahid ya kama hanya ba tare da bata lokaci ba ya nufo masallaci.

Kafin a yi Sallah ’yan Kalare sun cika harabar masallacin, a nan suka fara dukan ’yan uwa da suka soma zuwa. Shi Malam Usman Bello shi ma yana cikin masallacin, sai ’yan Kalaren suka fara dukansa da sanda, sai wani Bafade ya zo daga gidan Sarki ya ga ana dukan Shahid din, sai ya ce dan Shi’a ne ko? To, maza ku kashe shi! Daga nan ne fa sai wani ya daba masa wuka a wuya har wukar ta lume a ciki. Wani ya shaida mana cewa wani dan Kalare da ake ce wa Abdulmalik (Mali) dan unguwar kasuwar Mata Layin Najmuddin ne ya kashe shi.

An kashe Malam Usman Bello a gaban jami’an tsaro, sojoji da ’yan sanda. Bayan caka masa wukan ne sai ’yan sanda suka dauke shi jina-jina suka jefa shi a motarsu suka tafi da shi. A ran nan an raunata ’yan uwa 28. Daga baya sai aka bincika sai ba a ga Malam Usman Bello ba, aka yi ta neman sa amma ba same shi ba.

Washegari ranar Alhamis an je duk ofisoshin ’yan sanda, amma duk inda aka je sai su ce su babu kowa a hannunsu. Sai da aka shafe mako guda ana neman sa, amma shiru ba same shi ba. Sai a ranan Laraba, bayan mako guda da aukuwar al’amarin aka je mutuware na Asibitin Gombe ana cigiya. Sai masu jiran mutuwaren suka ce lallai akwai gawawwaki uku na wasu da ba a san masu su ba. Ana bude na ukunsu sai ga Shahid Usman Bello a kwance jini na zuba a jikinsa. Fuskarsa alamar yana murmushi, jikinsa bai kumbura, kafarsa sanye da takalminsa. Mai jiran mutuwaren Kirista ne, amma sai da ya yi mamakin yadda ya ga ga shi an kashe mutum mako guda, amma ga jini na zuba kamar a lokacin aka kashe shi.

An yi jana’izarsa ne ranar Juma’a 30/l2/2011 a kofar fada na Gombe, kuma har zuwa ranar Juma’ar jini bai daina zuba a inda aka soke shin ba, sai da aka samu auduga aka toshe wajen, kuma duk gabobinsa an jujjuya su kamar yadda ake yi wa rayayye, fuskarsa ta kara haske, hakoransa sun yi fari tas. An lullube shi da likkafani na Jaushanul Kabir da aka rubuta da Turbar Karbala.

Daruruwan mutane ne suka halarci Sallar Shahid din wanda Malam Muhammad Abbari ya jagoranta. ’Yan uwa daga Zariya, Kano, Darazo da sauran Da’irorin yankin Gombe da sauran al’ummar Musulmi suka yi Sallar. Bayan yin Sallar ne aka shiga sahu ’yan uwa maza da mata a yayin da Harisawa suke gaba suna buga badujala suna fareti suna wakokin yabon Shahidi, har aka je makabarta ta hanyan Bajoga wacce ta kai tsawon kilomita shida daga cikin gari, amma haka aka je da kafa cikin sahu.

Masu gadin makabartan sun ce su tun da suke ba su taba ganin jama’a haka sun rako wata gawa ba, kuma ba su san ana yi wa gawa gata ba sai a ranar. Malam Muhammad Adamu Abbari ya yi jawabi inda yake cewa lallai an kawo rayayye ne cikin matattu. Bayan gama binne shi ne dai sai aka nemi infaki a wurin inda aka tara sama da dubu 25 aka bai wa masu gadin makabartar duk albarkacin Shahid Usman Bello.

Malam Usman Bello dai ya yi shahada ya bar mace daya (Malama Hawwa) da yara shida: Adamu 16, Zainab 14, Yunusa 11, Fatima 8, Ali 5, da Hadiza 3, dukkansu suna Gombe.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan